Jummaʼa 9 Oktoba 2026 - 18:06
Sheikh Na’im Qasim Ya Gode wa Hauzar Ilimi ta Qum Bisa Aika Tawagar Malamai zuwa Lebanon

Hauza/ Babban Sakataren ƙungiyar gwagwarmayar Hizbullah, Sheikh Na’im Qasim, ya aika da saƙon wasiƙa zuwa ga tawagar da Hauzar Ilimi ta aika domin halartar bikin cika shekaru biyu da shahadar Sayyid Hasan Nasrullah da Sayyid Hashim Safiyuddin (Allah Ya yarda da su), inda ya miƙa godiya da yabo ga Hauzar Ilimi, shugabanta, malamai, ma’aikata da dukkan ɗaliban Hauza.

A cewar Sashen Ƙasa da Ƙasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal Muslimin Sheikh Na’im Qasim, Babban Sakataren ƙungiyar Hizbullah ta Lebanon, ya aika da wasiƙa zuwa ga tawagar Hauzar Ilimi da ta halarci bikin cika shekaru biyu da shahadar Sayyid Hasan Nasrullah da Sayyid Hashim Safiyuddin (Allah Ya jiƙansu), inda ya nuna godiyarsa ga shugabanci da dukkan masu alaƙa da Hauzar Ilimi ta Qum.

A cikin saƙon, Sheikh Na’im Qasim ya bayyana cewa Musulunci na asali na Annabi Muhammad (S.A.W.W.), tare da bin tafarkin wilaya da jagorancin Imam Khumaini (Allah Ya tsarkake ruhinsa) da Shahidin Jagora (Allah Ya ɗaukaka matsayinsa), su ne abubuwan da suka haɗa Hizbullah da Hauzar ilimi wuri guda.

Ya ƙara da cewa: “A yau ma, aiwatar da jihadi, gwagwarmaya, shahada da sadaukarwa a ƙarƙashin tutar jagorancin Waliyyul Amr, Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamenei (Allah Ya tsawaita rayuwarsa), bayan shahadar shahidanmu masu daraja, shi ne abin da ya haɗa mu da ku.”

Babban Sakataren Hizbullah ya yi nuni da yaƙe-yaƙe biyu na baya-bayan nan, wato ‘Uli al-Ba’s’, wanda ya biyo bayan shahadar Sayyid Hasan Nasrullah (Allah Ya jiƙansa), da kuma ‘Al-Asf al-Ma’kul’, wanda ya biyo bayan shahadar Shahidin Jagora (Allah Ya jiƙansa).

Ya bayyana cewa Hizbullah ta shiga yaƙi mai tsanani na tsawon shekaru biyu da ƙwayar cutar kansar da ake kira gwamnatin Sahayoniya, tare da dukkan laifuffuka da ta’asar da take aikatawa, da kuma azzalumin tsarin Amurka da ke bayanta.

Sheikh Na’im Qasim ya bayyana cewa Hizbullah ta yi tsayin daka da juriya bisa koyi da Imam Husaini (A.S.) da Sayyida Zainab (S.A.). Ya ce, da taimakon Allah, sun yi nasarar wargaza makircin maƙiyansu, kuma za su ci gaba da wannan tafarki cikin ɗaukaka da izza.

Sheikh Na’im Qasim ya kuma bayyana fatansa na samun cikakkiyar nasara ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Ya ce al’ummar Iran, rundunonin sojojinta, jami’an gwamnati, wanda yake a kan gaba cikinsu shi ne Shahidin Jagora tare da iyalansa, dukkan mayaka, malamai da kwamandoji, sun yi gwagwarmaya da dukkan ƙarfinsu, suka tsaya daram kamar dutse.

Ya danganta wannan fata da maganar Allah Ta’ala cewa:

«وَكَانَ حَقًّا عَلَيْنَا نَصْرُ الْمُؤْمِنِينَ»

Ma’ana: “Kuma ya kasance wajibi a gare Mu mu taimaki muminai.”

Babban Sakataren Hizbullah mai gwagwarmaya ya kuma tabbatar da cewa Hizbullah za ta ci gaba da wannan tafarki cikin tsayin daka da haƙuri. Ya jaddada cewa babu wani ƙarfi da zai iya girgiza Hizbullah, kuma idan suna tare da Allah, babu abin da zai faru face shiriya, dacewa da nasara.

A ƙarshen saƙonsa, Sheikh Na’im Qasim ya bayyana fatansa na kasancewarsu baki ɗaya cikin sojojin Imam Mahdi (A.F.), sannan ya aika da gaisuwa ga babbar Hauzar Ilimi ta Qum mai girma da gwagwarmaya, shugabanta, malamai, mataimakansa da ɗalibanta. Ya kuma yi addu’ar samun cikakkiyar nasara ga rundunonin Gwagwarmaya (Jabhatul Muƙawama).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha